Labarai

‘Jami’an tsaro su na barazanar kisa idan aka hana su cin hanci’

Jaipur, India (DABO FM) – Wasu daga cikin direbobin manyan motoci dake bin manyan titunan Najeriya, sun koka kan yadda suka ce jami’an tsaro a kan hanya suke tilasta musu bayar da cin hanci.

Sun ce lamarin ya kai makurar da ‘”Jami’an tsaron basa barinmu mu wuce har sai mun bada kudi, suna ce mana zasu kashemu kuma sun kashe banza.”

Direbobin sun bayyana haka ne cikin wani bidiyo da DABO FM ta samu wanda suka yi kira ga shugabannin tsaro da su dauki mataki, domin a cewarsu abin fa ya fara isarsu.

“A nan dai da kuka ga mun taru, guri ne na direbobi, mun yi wannan bidiyon ne domin yin korafi ga shugabannin gwamnati da na tsaro.”

“Ba wani abu bane, abubuwan da muke fuskanta a hanya, gaskiya ya ishemu, dalili kuwa shi ne, za ka dauko kaya, watakila za a baka baka N300,000, kafin ka tafi Arewa sai ka kashe N150,000 a bai wa jami’an tsaro. Har ta kai ga idan baka ba wa Soja kudi ba, zai ce ka koma gefe, idan ka kyalesu, zai ce sai ya harbeka babu abinda zai faru.

“Yanzu ya zama abu na dole sai ka ba wa dukkanin jami’an tsaro kudi, jami’an kula da shige da fice ne kawai basa karba suma saboda basa kan tituna ne.”

Duk da mai magana da wadanda suke tare a bidiyon basu fadi sunansu ba, sun yi kira ga shugabannin tsaro cewar tura fa kai bango.

“Har dukanmu ake yi, kuma ba barayi bane. Ko so ake yi mu zama ‘yan ta’adda ne ne? Munsan dama abinda kuke so kenan. Mun ada iyalai, dan kudi da ka rage zaka kai musu, jami’an tsaro sun karbe.”

Lamarin karbar cin hanci a manyan titunan Najeriya dai ya zama ruwan dare musamman saboda tsayuwar jami’an tsaron da na nufin bayar da tsaro.

Karin Labarai

UA-131299779-2