Me ke tsakanin Adam Zango da Hadiza Aliyu Gabon?

Karatun minti 1
Menene tsakanin Adam Zango da Hadiza Aliyu Gabon?
Jarumi Adam Zango da Hadiza Gabon

A cikin makon nan, alamu sun nuna akwai wata kyakkyawar alaka da take tsakanin taurarin fim na masana’antar Kannywood, jarumi Adam Zango da jaruma Hadiza Gabon.

DABO FM ta tattara yadda jarumi Adam Zango ya wallafa kalaman birgewa da kwantar da zuciya ga jaruma Hadiza Gabo inda har ya rubuta cewa “Ba zan taba barinki ba.” Itama jarumar tana martani da kalamai masu nuna aminta da zancen Adam Zango.

Sai dai tambayar da ta tsaya a ran masoyan taurarin bai wuce cewar mene a tsakanin jarumawan biyu ba duk da cewa akwai makamanciyar alakar tsakanin jaruma Gabo da mawaki Nazir M Ahmad ‘Sarkin Waka.’

Cikin kwana 4, tin daga ranar Asabar, Adam Zango ya wallafa bidiyon Hadiza tana rera wata waka, jarumin ya wallafa bidiyon tare da furucin, “Kamar ni Hadiza Gabon take tunawa, kar ki damu ba zan taba barinki ba.” Jarumar tayi martani tace; “Sosai Kam.”

A ranar Litinin, jarumin ya sake sanya hoton jarumar inda ya kira ta da ‘Crush’ ma’ana wacce take burgeshi ko kuma yake So (ba na soyayya ba). A nan ma jarumar tayi martani da “Ina sane da kai.”

Kazalika ranar Talata da Laraba, jarumin ya sake wallafa jarumar a shafinsa na Instagram, ya kuma ce “Waye ba ya son abu mai kyau.”

A shekarun baya dai taurari biyun sun kasance makusantan juna inda suka rika fitar da fina-finan tare irinsu Basaja, Aci Bulus, Matar Manga, Alkibla da sauransu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog