Labarai

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Bauchi ya kamu da Corona Virus

Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da kamuwar gwamnan jihar, Bala Muhammad da cutar Corona Virus.

Hakan na zuwa ne bayan gwaji da akayi bisa bayan mu’amalarshi da dan gidan Atiku Abubakar wanda a ranar Litinin aka tabbatar da yana dauke da cutar.

Sanarwar na kunshe a cikin wata sanarwar da DABO FM ta samu wacce mataimakin gwamnan a fannin labarai, Mukhtar M. Gidado a yau Talata.

Sanarwar tace hukumar kula da cututtukan Najeriya NCDC tayi wa gwamnan tare da iyalinshi da mataimakanshi gwajin cutar bayan sun hadu da dan gidan Atiku Abubakar.

“Sakamakon gwajin da akayiwa gwamna Bala Muhammad, iyalanshi da mukarrabanshi guda 6 ya fito.”

“A cikin gwajin da akayi guda 6, guda daya ya tabbatar da cutar COVID-19 wanda shi ne na gwamna Bala Muhammad.”

UA-131299779-2