Kai tsaye

Kai Tsaye: Yadda al’umma a Kano suka ki fitowa zaben kananan hukumomi

dakikun karantawa

Rahotan yana zuwa ne kai tsaye, a rika sake loda shafin domin sabuntawa.

JAIPUR INDIA: A yau Asabar, 16 ga watan Janairun 2021 ne ake kada kuri’ar zaben shugabannin kananun hukumomi da kansiloli a jihar Kano.

Sai dai wani abin ban mamaki shi ne yadda al’ummar birni da kewaye suka ki fito su kada nasu kuri’un.

A wani zagaye da DABO FM ta kai wasu daga rumfunan zaben wasu kananan hukumomi a tsakiyar birnin Kano, ta tabbatar da cewa al’ummar yankunan basu fito kada kuri’ar ba.

Kazalika wasu rahotanni da ga wasu kafafen yada labarai sun nuna yadda yara ‘yan kasa da shekara 10 suka karade wuraren kada kuri’un a wasu kauyukan jihar ta Kano.

DABO FM ta ziyarci makarantar Kano Teachers College da ke gaabashin Fagge, a karamar hukumar Fagge, in da muka iske turawan zabe a zazzaune ba tare da mutanen da za su kada kuri’ar ba da misalin karfe 01:20 na rana.

A mazabar Fagge D1 Kofar Gidan Mai Unguwa, duk dai a karamar hukumar Fagge, DABO FM ta tattabar da rashin halartar masu kada kuri’a a akwatunan.

An samu fitowar jama’a kadan a mazabar Gwammaja Makarantar Ibrahim Yaro Yahaya da ke karamar hukumar Dala.

A mazabar Kofar Mazugal, mun zanta da wasu shugabannin jami’iyyar APC na mazabar. Sun bayyana kokensu kan yadda suka ce manyan jami’iyyar sun hana su wasu kayyakin walwala da jami’iyyar ta bayar domin su samu kwarin gwiwar gudanar da aikin zaben.

Wata ‘yar jami’iyyar APC da ta nemi mu sakaye sunanta, ta zargi wasu jagororin jami’iyyar da ‘danne’ musu kudade, a cewarta, kamar yadda za ku iya gani a shafinmu na Facebook.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog