0
Wani Jami’in Sojan Sama a Najeriya, ya mayar da €37,000, kwatankwacin Naira N15,043,211.46 da ya tsinta a wata Jaka a sansanin mahajjatan jihar Kano.
Jami’in da aka bayyana da Bashir Umar, ya tsinci kudin ne a dai dai lokacin da suka fito rangadi tare da abokan aikinshi a ranar Lahadi.
DABO FM ta binciko cewa jami’in sojan dai ya kira lambar dake jikin kwalin da aka sanya kudin domin neman asalin mai kudin wanda aka bayyana da Alhaji Ahmad.
Tini dai rundunar Sojan Sama da kasa ta hannun mai hulda da jama’a a rundunar, Kwamanda Ibikunle Daramola, tace shugaban Hafsin sojin ya bayar da umarnin karrama Bashir Umar.
