Labarai

Sabon Bankin Musulunci ‘Taj Bank’ yana neman ma’aikata a Abuja da Kano

Sabon Bankin Musulunci ‘Taj Bank’ ya fara neman ma’aikata a sabbin bankunan dake birnin tarayya, Abuja da jihar Kano.

Bankin yazo da sabon salo inda ya bukaci yin aiki da matasa masu shekaru 20 zuwa 30.

Bankin ya kasafta bangarorin guraben ma’aikatan zuwa kashi 3.

Ga jerin rukunan tare da dukkanin abinda ake bukatar mai neman aikin ya kasance ya/ta na dashi.

Rukunin Ma’aikata masu kula da jin dadin Abokan Ciniki;

Matakin Karatu: Bsc (2:2)

Shekaru: 21-35

Ya kasance akwai kwarewa.

Rukunin Ma’aikata masu kula da sha’anin ‘Teller’:

Matakin Karatu: OND/NCE

Shekaru: 20-30

Akwai yiwuwar fin samun dama ga wandanda suke da kwarewa.

Rukunin ‘Transaction Officer’

Matakin Karatu: HND, Bsc (2:1, 2:2 da 3)

Shekaru: 21-35

Ana bukatar mai kwarewa.

Ga duk masu sha’awar neman aikin, zasu iya tura takardunsu ga adreshin email na ‘pait.recruit@gmail.com kafin ranar 31 ga watan Yulin 2019.

Karin Labarai

Masu Alaka

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi za ta dauki sabbin Ma’aikata

Dabo Online

Mutane 50,000 sun nemi aikin koyarwar da ake neman mutane 1000 a jihar a Lagos

Dabo Online

Daukar Aiki: Kamfanin Dangote da Abdussamad BUA suna neman sabbin Ma’aikata

Dabo Online
UA-131299779-2