Jam’iyyar PDP a jihar Jigawa ta fada cikin rikici

Tin bayan gudanar da babban zaben 2019 da jam’iyyar APC ta lashe baki dayan akwatunan jihar, Yanzu haka rikicin boye ya fara fitowa fili.

Tun a wancan lokacin jam’iyyar ta dare gida Biyu, in da bangaren Dan takarar Gwamnan jihar Malam Aminu Ibrahim Ringim ya kama Tuwansa da ban, wanda da yake hade da mai gidansa tsohon Gwamnan jihar, kuma uba a jam’iyyar a kasa, Alh. Sule Lamido.

Yau an wayi gari zagin jam’iyyar na PDP sun yi taruka a wasu daga cikin kananan Hukumomin jihar domin nuna kin jinin ci gaba da yiwa Alh. Sule Lamido biyayya.

Tarukan da aka gudanar a kananan Hukumomi irin su; Dutse, Hadejia, Gwaram da ma wasu yankunan, sun ce ba za su ci gaba da biyayya wa Sule Lamido ba, domin a hangen su zagon kasa yake yi wa jam’iyyar.

Masu Alaƙa  Sule Lamido ya caccaki Obasanjo akan sukar Musulunci da 'Yan Fulani

A bangaren Sule Lamido, binciken wakilin mu na jihar Jigawa, Rilwanu Labashu Yayari yayi nuni da cewa, Alh. Sule Lamido shi ne, wanda yayi ruwa yayi tsaki na ganin an baiwa Malam Aminu Ibrahim Ringim takara har karo 2.

Ana ganin cewar a shekarar 2015 Sule Lamido yayi uwa da makarbiya, tare da yin abinda za’a iya cewar turtasa baiwa Aminu Ringim goyon bayan idan ana son cigaba da zama a jami’iyyar. Haka akayi, wasu suka zauna wasu suka fice. Shekarar 2019, ana zargin an sake maimai wajen fidda Aminu Ringim sake tsayawa takara.

Yanzu haka dai, hankalin mabiya jam’iyyar ya koma ga zabukan shugabanin jam’iyyar da za a gudanar cikin wannan shekara, in da kowane bangare yake son ace shugabanin nasa ne.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.