Labarai

Wani malami ya maida kyautar motar da dan majalisa ya bashi, ya bukaci a tallafawa talakawa

Babban limamin masallacin Ansar – Ud – Deen Society, Sheikh Ahmad Abdurrahman ya ki karbar kyautar mota kirar Toyota Sienna daga dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Mushin II dake jihar Ikko, Hon. Bolaji Yusuf Ayinla.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa babban limamin ya maida wa Wanarabul Bolaji kyautar motar da ya aike masa domin yin harkokin addini da ita, sai dai shehun malamin yace ya dawo da ita ne cikin girmamawa tare da kiran dan majalisar da ya ci gaba da tallafawa talakawa kamar yadda ya saba.

Bayan wa’azi mai ratsa zuciya, Sheikh Ahmad yayi addu’a ga dan majalisar Allah ya saka masa da mafificin alkhairi tare da godiya marar adadi, bayan haka yayi wa Najeriya addu’ar karuwar arziki da zaman lafiya baki daya. Kamar yadda jaridar iWittness ta ruwaito.

Karin Labarai

UA-131299779-2