Mun sa Kwankwaso ya ajiye siyasa da karfin tuwo – Ganduje

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa yayi wa tsohon mai gidan sa kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ritaya da karfin tuwo a siyasa.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa gwamnan yayi wannan batu ne lokacin da ya karbi bakoncin shugaban majalisar jihar kano, Abdulaziz Garba Gafasa tare da sauran yan majalisar dokokin jihar domin rakiyar sabbin yan majalisar da sukayi nasara a zaben mai-mai da aka gabatar a karshen watan Junairu.

Jam’iyyar APC a jihar Kano dai ta samu gagarumar nasara a zabukan da aka gabatar, inda ta lashe kujeru 6 cikin 7 da aka sake zaben nasu.

Ganduje ya kara da cewa “Nasarar ta Jam’iyyar APC ta tabbatar da yiwa Kwankwaso ritaya a siyasa baki daya, ‘yan shekaru kadan baya yace [Kwankwaso] zai yiwa shugaba Muhammadu Buhari ritaya tare dani amma yanzu idan aka duba wa akayi wa wannan ritayar?”

Masu Alaƙa  Katsina: Gidauniyar Kwankwasiyya zata kafa asusun fitar da dalibai karatu kasashen Duniya

Da yake bayyana yadda Jam’iyyar APC ta rasa kujerar Kiru da Bebeji, Ganduje ya bayyana cewa “Bamu samu nasara a kujera u Kiru da Bebeji ba saboda rikicin cikin gida na da muke fama dashi wanda dan majalisar tarayya na rigima da shugabancin jam’iyya na karamar hukuma.”

Abdulmumin Jibril Kofa dai shine dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Kiru da Bebeji wanda yasha kayi a hannun Ali Datti Yako na jam’iyyar PDP, sai dai ansha dambarwa domin ana ganin jam’iyyar APC dince da kanta ta tade Kofa domin rigimar sa da shugaban Jam’iyyar, Abdullahi Abbas.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.