Labarai

Jimami: Gobara ta lamushe gidan mai na Aliko dake Tarauni a Kano

Tin cikin daren jiya misalin karfe 12 na dare wuta ke faman ci a gidan mai na Aliko Oil dake tarauni kan titin Maiduguri.

Dabo FM ta zanta da shaidar gani da ido a dai dai wannan lokaci da wutar ke ci kamar wutar daji, Malam Sanusi Garko ya shaida mana cewa “Yanzu haka ina hango yadda wutar keci duk da ina nema amma ba nisa tsakanin mu.”

Wannan ya afku ne cikin daren Asabar misalin 12 na dare, wutar dai ta kone gidan man kurmus, daji kashan anyi asarar miliyoyin dokiya sai dai zuwa yanzu Dabo FM bata samu rahoton rasa rai ba.

Karin Labarai

UA-131299779-2