Labarai

An zargi wanda ya kamu da Kwabid-19 a Kano da shigar da cutar da ‘ganganci’

Al’ummar jihar Kano sun bayyana rashin jin dadinsu biyo bayan wasu rahotanni da suka nuna wanda ya kamu da cutar ya shigar da ita cikin jihar bisa ganganci.

A jiya ne dai aka samu bullar cutar Kwabid-19 ta farko a jihar Kano.

Bisa binciken kwafar da wasu ‘yan jarida suka gudanar ciki har da Nasiru Zango na gidan rediyon Freedom dake Kano, sun gano yadda mutumin ya shigo cikin Kano da sanin yana dauke da cutar.

DABO FM ta tattara cewar sun bayyana cewar anyi masa gwaji bayan bullar alamomin cutar, ya kamo hanyarshi zuwa Kano duk kuwa da dokar hana shige da fice da gwamnatin jihar ta sanya.

Hakazalika bayan shigowarshi Kano, ciwon ya kara tsanani inda ya zargaya wani asibitin kudi a jihar, yayi jinya ba tare da yayi bayanin wancen gwaji da akayi masa na cutar ta Kwabid-19 ba.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Kano ta bakin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewar mutumin yayi mu’amala da mutane da dama tin bayan dawowarshi cikin jihar.

“Wannan da ya kamu da wannan ciwo, yaje Abuja, Lagos da Kaduna

“Babban aiki da yake gabanmu shine a tabbatar cewar duk wandanda sukayi hulda da mu’amala da wanda ya kamu da wannan ciwo, lallai da lallai sai anga yawan wadanda sukayi mu’amilla dashi.”

Gwamnatin ta tabbatar da zuwanshi daurin aurarraki da masallacin Juma’a.

Sai dai al’ummar Kano sunyi matukar bakin ciki jin yadda mutumin da yake tsohon jakadan Najeriya ya ‘kwaso cutar da saninshi ya shigo da ita Kano.’

Daga kafafen sadarwa zuwa masu bayyana ra’ayoyi ta fatar baki, sun bayyana gwamnati tayi masa hukunci mai tsauri domin sun bayyanashi a matsayin ‘mamugunci.’

Karin Labarai

Masu Alaka

Likitoci guda 10 a Kano sun kamu da cutar Kwabid-19

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutane 29 sun sake kamuwa da Koronabairas a Kano, jumillar 342

Dabo Online

‘Babu ranar dawo da cibiyar gwajin Kwabid-19 dake Kano’

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutane 12 sun sake kamuwa da Kwabid-19 a Kano, jumilla 21

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Ganduje ya amince da bude masallatan Juma’a da Sallar Idi a Kano

Dabo Online

Duk da dokar hana fita, an gudanar da Sallar Juma’a a Kano

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2