Home Kiwon LafiyaAn samu mai Covid-19 na farko a Kano

An samu mai Covid-19 na farko a Kano

by Dabo Online
0 comments

An samu mai dauke da cutar Covid-19 na farko a jihar Kano bayan fitowar gwajin a ranar Asabar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya tabbatar da hakan, sai dai bai yi cikakken bayani ba.

Sai dai babban mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, ya tabbatar da batun bullar cutar a shafinshi na Twitter.

“An samu mai dauke da Covid-19 na farko a jihar Kano.”

Ya bayyana cewar tini dai akayi wa makusantan mutumin gwaji wanda a yanzu haka ana jiran sakamako.

“Yanzu haka yana cibiyar da aka ware domin killace masu dauke da cutar dake Kwanar Dawaki a jihar Kano.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00