Jirgin rundunar Sojan Sama ta Najeriya ya tashi domin zuwa kasar Zimbabwe domin kai musu kayayyakin tallafi biyo bayan ambaliyar ruwa da ta faru a kasar.
Mai magana da yawun rundunar, Air Com. Ibikunle Daramola ne ya sanar da hakan a ranar Asabar a ofishinsa dake Abuja.
DABO FM ta binciko cewa; Za’a baiwa mutanen da iftila’in ambaliyar ruwan da akayi a watan Afirilu kayayyakin, kamar yacce rundunar ta bayyana.
Rundunar tace shirin bayarda kayayyakin tallafi yana karkashin Hukumar dake kula da bada Agajin Gaggawa ta kasa.
Kayayyakin sun hada da magunguna, gidajen sauro, da sauran dangogin kayayyakin lafiya domin ragewa wadanda iftala’in ya fadawa radadi.
Yace jirgin rundunar mai lamba, C-130H ya tashi daga filin tashi da saukar jirage na Nmadi Azikwuwe dake birnin Abuja, zai kuma sauka a filin jirgin sama na Robert Gabriel Mugabe dake birnin Harare na kasar Zimbabwe
