Jirgin zuwa duniyar Wata na Indiya yayi tutsu, sakanni kadan daya rage sauka a kudancin duniya

Bayan shafe kwanaki 55 da Jirgin zuwa duniyar wata mai taken ‘Chandrayaan II’, jirgin yayi tutsu.

DABO FM ta binciko cewa masu kula da jirgin sun rasa na’urarshi a lokacin daya rage saura kilomita 2.51 jirgin ya sauka a inda ake so.

Kasar Indiya dai ta harba jirgin ne tin a ranar 13 ga watan Yulin 2019, maka daya bayan fasa harba jirgin a shirin harbashi na farko.

An saita saukar jirgin a daidai karfe 1:53 na dare zuwa 2:30 na dare a agogon kasar Indiya.

Mista K. Sivan, daraktan hukumar ISRO, ne ya sanar da batan na’urar sadarwa tsaknin jirgin da masu tafiyar da aikin jirgin.

Masu Alaƙa  Wani mutum ya shiga gasar cin kwai 50, ya mutu bayan cinye 41 akan N10,000

“Komai yana tafiya kamar yacce aka tsara, a dai dai lokacin da ya rage saura kilomita 2.51 jirgin ya sauka, muka rasa na’urar sadarwa.

Firaministan kasar, Narendra Modi, yayi kira da masana kimiyyar dake cikin tsarin tafiyar da hukumar ta Indiya, su kwantar da hankalansu akan rashin nasarar da aka samu.

Kasar ta kudiri niyyar zama kasa ta farko da ta fara harba jirginta domin sauka a kudancin wata tare da dauko hotunan duniya daga kudancin.

Har yanzu dai kasashen China, Amurka, Rasha ne suka sami nasarar aikewa da nasu jirgin, sai dai suma iyakarsu sashin arewaci da tsakiyar watan.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.