Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya rarraba motocin cigaba da gudanar da aiki ga Jami’an tsaro da hukumar kare cunkoson ababen hawa a jihar Zamfara.
DABO FM ta binciko cewa; Gwamna Matawalle ya rarraba motocin ne a rana ta biyar da ake bikin cikar gwamnatin kwanaki 100 da kama aiki.
Jami’an tsaro na ‘yan sanda, ‘Yan sa kai, Asibitoci da hukumar ZAROTA ne suka amfani da sabbin motocin da gwamnan ya rarrabawa.
Hakazalika, gwamnan ya sake karbar wasu tubabbun masu tada zaune tsaya wanda suka tayar da hankalin jihar Zamfara, wadanda suka ajiye makamansu a yau Juma’a, 6 ga watan Satumbar 2019.
An dai karbi makaman ‘yan Bindigar ne a wajen taron tare da danka su ga jami’an tsaro.
