Wasanni

Juventus ta lashe Super Coppa karo na takwas

Kungiyar dake jan ragamar teburin gasar Serie A ta kasar Italiya ta samu damar lashe kofin Super Coppa karo a takwas.

Kungiyar ta samu nasarar wasan ne yayin da dan wasa Cristiano Ronaldo ya gefa kwallo a minti na 61 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Wannan shine karo na farko da dan wasan ya samu damar lashe wani kambu a kasar ta Italiya. Da yake bayyanawa a shafinshi na Instagram , Cristiano Ronaldo ya bayyana farin cikinshi da wannan al’amari kuma yayin fatan samu wasu dayawa.

Juventus ce kungiya daya tilo da batayi rashin nasara ko daya ba a wasanninta na gasar Serie A.

Masana na ganin kungiyar zata iya lashe gasar ta Serie A a karo na takwas a gere.

Karin Labarai

UA-131299779-2