Atiku Abubakar ya dau hanyar zuwa kasar Amurka

Dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam’iyyar PDP ya kama hanyar zuwa kasar Amurka.

Atiku Abubakar ya bar kasar Najeriya yau da safe zuwa birnin Washington D.C babban birnin kasar Amurka, majiyar tace daga yanzu zuwa kowane lokacin Atiku zai iya sauka a kasar.

Tin 2007 Atiku bai kara zuwa kasar ta Amurka ba wanda yakai shi shafe shekaru goma sha biyu.

Rahotan da jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa tace, Atiku zai bayyana a wani taro na ‘yan kasuwa a birnin Washington D.C tare da gudanar da wasu tarurruka da zasu taimaka masa wajen yakin neman zaben da yake yi.

Masu Alaƙa  Atiku zai fuskanci matsin lamba inya dawo Najeriya - Lai Muhammad

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.