Zababben Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa yana nan da ranshi kuma babu hatsarin daya ritsa dashi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da masoyanshi a daren yau Juma’a 23/03/19 a babbar birnin jihar ta Kaduna.
“Ina so in godewa muku da kuka samu halartar wannan taro, ina so in jaddada kuma in tabbatar cewa Ina nan a raye, kuma babu wani hatsari daya ritsa dani.”
“Ina so in kara gode muku da kuka fito kukayi zabe.”
A kwanakin baya, wasu kafafen yada labarai na yanar gizo-gizo suka rika bayyana rahotanni cewa Gwamnan yayi hatsari, ya rasu tare da direbanshi.