Kano: Cin Hanci: Ganduje ya rabawa wasu ma’aitakan INEC filaye

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta rabawa wasu daga cikin ma’aikatan hukumar zabe ta INEC filaye a jihar Kano.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito daga wasu majiyoyin sirri da sukace Gwamna Ganduje ya saka hannu domin a rabawa ma’aikatan filaye, a dai-dai lokacin da ake shirin zake zabe a gobe Asabar.

Tin a ranar 5 ga watan Fabarairu aka bankado wasu takardu da suke nuna filayen da Gwamnan ya sahale a baiwa ma’aikatar zaben.

Daga cikin takardun da jaridar ta bankado, an ga inda gwamna ya baiwa Sakataren ma’aikatar kasa da safiyo ta jihar Kano umarni a zartar da bada filayen cikin gaggawa.

Daga cikin wuraren da Gwamnan ya sahale a bayar akwai a garin Bandirawo, Umarawa da sauran gurare.

Daily Nigerian ta so jin ta bakin shugaban hukumar kasa da safiyo na Kano, Yusuf Danduwa, amma hakan ya gaza cimma ruwa domin yaki daga waya kuma yaki maido da sakon karta kwanar da aka aike masa dashi.

A gobe Asabar ne dai ake sa ran cigaba da gudanar da zaben Gwamna a jihar Kano tin bayan da hukumar zabe ta INEC ta bayyana zaben ranar 9 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.

%d bloggers like this: