Kaduna,Abuja: Kudin aikin Hajji na bana, Naira miliyan 1.5 – Hukumar Alhazai

Hukumar alhazai reshen jihar Kaduna da babban birnin tarayyar ABuja, sun bayyana naira miliyan daya da rabi a matsayin kudin aikin hajjin bana.

Hukumar, reshen jihar Kaduna ya bayyana sanarwar ne ta hannu mai hulda da mutanenta, Malam Yunusa Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a jihar Kaduna.

Malam Yunusa yace; babban hukumar aikin Hajji ta Najeriya,’NAHCON’ ta aminta da tsabar kudi na Naira biliyan N1,549,297.09 a matsayin kudin aiki Hajji 2019 wanda mahajjatan jihar KAduna zasu kashe.

DaboFM ta tattaro bayanai da suka nuna cewa, an cire kudin ne bayan kammala lissafin dukkanin abinda mahajjatan zasu bukata hadi da masaukin su a garin Makkah da kuma garin Madinah.

Abdullahi ya ce dalar Amurka 800 ce a matsayin alawus na tafiya ”BTA”ga mahajjatan.

Ya kara da cewa, wadanda suka halarcin Hajjin bara ko shekaru 4 da suka wuce, zasu kara Riyal 2000, kwatankwacin Naira 162,000, akan kudin da aka fitar.

Daily Trust ta rawaito cewa, kusan mahajjatan Kaduna na bana, su rika sun fara biyan kudaden su, wanda wasu suka biya N800,000, wasu kuma Miliyan 1.5.

Mallam Abdullahi yace; “Kowanne mahajjaci ya tabbata ya karbi takardar banki a karamar hukumar su kafin su kai ga biyan kudaden.

%d bloggers like this: