(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

In Sarki ya kira dan siyasa mutumin kirki, masu hamayya zasu ce yana goya masa baya – Dr Pantami

dakikun karantawa

Sheikh Dr Isa Ali Pantami, daraktan hukumar NITDA, yace yazamewa ‘yan siyasa dole su rika girmama sarakunan gargajiya saboda irin amfanin da suke yiwa al’umma.

DaboFM ta tattara bayanai a wata ganawa da malamin yayi da Jaridar Daily Trust, inda yayi ga shugabanni da kuma bada dalilan da yasa ya zama tilas a girmama sarakunan gargajiya.

Majiyoyin DaboFM sun bayyana Sheikh Pantami ya amsa tambayar da wakilin Daily Trust ya masa kamar haka; Yawanci ‘yan siyasa suna kallon sarakunan gargajiya a matsayin masu zabar bangare lokutan siyasa. Kana ganin hakan yana da nasaba akan rikicin dake shiga tsakaninsu?

DaboFM ta rawaito Malam ya bada amsa kamar haka; “Kowanne dan Najeriya yana da ikon yin wanda yake so idan aka zo batun jagoranci. Naji ana ta fadar haka, amma a nawa bangaren, duk wadanda (Sarakunan) dana sani basa nuna bangaranci kamar yadda ake yada jita-jita.”

Sheikh Pantami yayi nuni da cewa, “mafiya yawan Sarakuna ana zarginsu da bin ra’ayin wani a siyasa ne saboda, da zarar an kawo musu ziyara, in suka karbi mutum hannu bibbiyu, suka yaba masa, tare da cewa masa mutum na kwarai.”

Mutanen wanda suke neman matsayi iri daya dashi, zasu fara yadawa cewa Sarki yana yin wani. Yabon mutum baya nuna cewa ana yin shi bane.

“Yan siyasa sune aikewa da sakon kawo zuwa masarautu, kowa ana tarbarshi. Ka taba jin inda wata masarauta ta hana wani dan siyasa kawo ziyara.”

“Duk da cewa sarakuna basu da wani karfin iko, amma sun kansu ‘yan siyasar sun san cewa mutane sunfi ganin girman sarakunan akansu.”

“Mu a Arewa, sarakuna sune shuwagabannin mu, musamman ma ta fuskar addini.”

“Dole mu girmama su, ko min matsayin mu, a jagorantar addini, ko matsayinmu a gwamnatoci jihohi, ko ma menene dai.”

“Muna girmama su koyaya shekarunsu suke, iyayenmu ne, kuma shuwagabannin mune, saboda shuwagannin addini da sarakuna ba’a girmama su saboda shekaru sai dan matsayin da suke kai.”

Sheikh Pantami ya kara da cewa Sarakuna sune suke iya samun kowana irin bayanai da suke faruwa a garin hatta dana matsalar tsaro, domin sunfi Jami’an tsaro samun rahotanni akan lamuran gari da tsaro.

“Duk sakon da kaje dashi gaban Sarki, ko baka sameshi ba inka fada a fada, lallai za’a fada masa.”

“Ya zamana tilas, yan siyasa su girmama sarakunan mu, wasu suna iya kokarinsu, amma wasu basayi ko kadan, kamar yadda muke samun labari.

Gargadi

Ba’a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta [email protected]Karin Labarai

Sabbi daga Blog