Kamfanunuwa hako ma’adanai a Zamfara sun fara bankwana da ma’aikatansu ‘yan kasashen waje bisa umarnin Gwamnati

dakikun karantawa

Kamfanunuwa dake aikin hako ma’adanai a jihar Zamfara sun fara sallamar ma’aikatansu ‘yan kasashen waje.

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan Gwamnatin Najeriya ta bawa duk wani ma’aikacin dan kasar waje kasa da awa 48 domin ficewa daga jihar ta Zamfara.

Kamfanin ISS-HASS NIGERIA LIMITED, hannu mai kula kamfanin, Alhaji Abubakar Hassan ya tabbatar mana da bankwanan da sukayi da wasu daga cikin ma’aikatansu yan asalin kasar China.

A zantawar da mukayi dashi, Alhaji Abubakar Hassan ya shaida mana cewa sunyi haka ne domin bin umarnin gwamnatin tare da tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar Zamfara dama Najeriya baki daya.

Jihar Zamfara dai ta shiga wani matsanancin hali inda ‘yan bindiga suka addabi garin baki daya ta hanyar garkuwa da mutanen gari, yin harbi kan mai uwa da wabi, tare da yiwa mata da kananan yara fyade a bainar jama’a.

A yan satuttuka da suka gabata, a karamar hukumar Shinkafi yan bindigar sun kashe mutane kimanin 48 a kauyukan Kurya da Kursawa da makotansu.

Hakan ya janyo cece kuce a bakin al’umma musamman rashin nuna alhini da shugaba Muhammadu Buhari akan kashe kashen da akeyi.

Hakan yasa kungiyoyi daban daban suka fara zanga zangar lumana tare da kiran gwamnati musamman ta jihar Zamfara, ta dau matakin daya dace wajen dakile kashe-kashen.

Sai dai a rufucin da shugaba Buhari yayi, yace  “Rashin adalci ne ace ban damu da kashe kashen Zamfara ba” hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan an fara zanga zanga a kasa dama kasashen waje.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog