Kano: Ganduje zai biya wa dalibai 38,632 kudin NECO, ya gargadi makarantu akan karbar cin hanci

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje tace zata biyawa daliban jihar Kano kudin jarrabawar NECO.

Hakan na zuwa ne bayan da akayi faduwa jarrabawar “Qualifying”, wacce gwamnatin jihar ke shiryawa domin tallafawa daliban sakandire wajen biya musu kudin jarrabawar kammala sakandire idan sun samu nasara.

Da yake bayyanawa a wata sanarwa daya fitar, kwamishan yada labaran jihar Kano, Mallam Muhammad Garba, ya shaida matakin da Gwamnatin ta dauka na biya wa daliban jarrabawa a matsayin sabon tsarin da suka fito dashi.

Malam Garba yace gwamnatin zata kashe N424,952,000.00 wajen biyawa daliban guda 38,632 akan kudin N11,000 kowanne dalibi.

Gwamnatin  ta gargadi shuwagabanni makarantu dasu guji karbar kudade game da jarrabawar daga hannun dalibai.

Ya shaida cewa akwai tsare tsare masu inganci da kyau wanda zai baiwa kowa damar yin karatu cikin sauki.

 

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog