KANNYWOOD: Amina Amal ta nemi Hadiza Gabon ta biyata diyyar Miliyan 50 a Kotu

Karatun minti 1

Matashiyar Jarumar Kannywood Amina Amal ta mika jaruma Hadiza Gabon gaban kuliya manta sabo.

Jaridar Leadership Hausa ta rawaito cewa Amal ta nemi Hadiza Gabo ta biyata diyyar Naira Miliyan 50 bisa tuhumar ta da ci mata zarafi.

[the_ad id=”5121″]

“Wannan bayani ya na kunshe ne a cikin takardar kara, wacce wasu lauyoyin kare hakkin bil’adama guda 15 su ka shigar a babbar kotun tarayya da ke Kano a madadin ita Amal din.” -Leadership

Lauyoyin dake kare muradin Amina Amal sun sun nemi kotu ta haramtawa Hadiza Gabo sake lakada duka, takura ko matsin lamba ga Amina Amal a nan gaba.

Har ila dai, lauyoyin sun nemi kotu data hukunta Hadiza Gabon domin daukar darasi.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog