Labarai

KANNYWOOD: An kira marin da Hadiza Gabon tayiwa Amal cin zarafin ‘Dan Adam

Duk Wanda yabawa Hadiza Gabon shawara tayi wannan bidiyon kuma ta bari duniya tagani ya cuceta.

Acikin abinda yafaru tsakanin Gabon da Amal babu wani waje da Amal din ta kama sunan Hadiza Gabon, kuma tabbas hakane, amma me yasa Gabon ta tabbatar cewa da ita ake?

Menene dalilinta?

Misali idan wani yazo yace kana shan giya kuma kasan baka shan giyar akanme zaka damu kanka? Musamman ma idan babu Wanda yasan lokacin da kukayi maganar?

Yanzu Gabon tayi bidiyo tana dukan Amal duniya tana gani kuma Amal ta amsa cewa tayi laifin.

Daga  baya Amal zata iya zuwa kotu ta nemi hakkinta kuma tace dukanta akayi shine yasa tun farko ta amince da laifinta.

Hadiza Gabon dole tanada wasu mutane wadanda basa shiri ko kuma suke riguma, zasu iya amfani da wannan al’amarin  domin cin mutuncinta a kotu.

Matsalar ba kawai tsakanin Gabon da Amal bace dole sai wasu sun shiga, musamman masu neman rigima da Gabon din.

Yanzu duniya zata sake sanin abinda yake faruwa a Kannywood sannan kuma duk wani zargi da akeyi akansu zai tabbata.

Hadiza Gabon ba ‘yan Nigeria bace itama yarinyar Amal, yar Kamaru.

Sahalewar

Abba Ibrahim Gwale

 

Kiranta: [irp posts=”7213″ name=”Gobara a KANNYWOOD: Hadiza Gabon ta mammari Amina Amal, bisa zarginta da neman yi mata lalata”] domin jin cikakken abinda ya faru.

Karin Labarai

UA-131299779-2