Shugaban KASa Sudan, Omar Al-Bashir, yayi murabus daga mukamin shugabancin kasar.
Hakan na zuwa ne dai dai lokacin da ‘yan kasar suka shafe tsawon dare biyar suna gudanar da zanga-zanga a kasar.
Zanga zangar data shiga tarihin kasancewar ta wacce ba’a taba tara mutane a zanga zanga irin wannan a kaf fadin Afrika ba.
Yanzu dai Al Bashir ya mika mulkin ne zuwa rundunar sojin kasar bayan shafa sama da shekaru 29 yana mulkar kasar.