Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kano: Hukumar INEC ta dage zaman tattara sakamako zuwa 8 na safiyar Lahadi

1 min read

A cigaba da tattara sakamakon zaben wuraren da aka sake zabe a jihar Kano, INEC ta dage zaman zuwa 8 na safiyar Lahadi, 24/03/19.

Baturen zaben ya bayyana hakan ne bayan cimma matsaya da wakilan jami’iyyu bisa rashin kawo wasu kananan hukumomi.

Hukumar ta tsayar da tattara sakamakon da karfe 1 na daren Asabar.

Ana dai dakon isowar sakamakon mazabar GAMA ne dake karamar hukumar Nassarawa.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.