0
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta bayyana cewa ta sanya ranar da za a gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a faɗin jihar baki ɗaya.
Rahoton Dabo FM ya bayyana shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bada sanarwar a babban ofishin hukumar dake jihar Kano.
Farfesa Sheka ya bayyana cewa za’a gudanar da zabukan a ranar 16 ga Junairu 2021.
Ƙarin bayani na nan tafe..
