Ruguza SARs matakin farko ne na yi wa rundunar ‘Yan Sanda garambawul – Buhari

Karatun minti 1
President Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ruguza jami’an ‘yan sanda masu kakkabe ayyukan fashi da makami na SARS a matsayin mataki gwamnati na farko don gyara ga rundunar ‘yan sanda.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Litinin.

Hakan na zuwa ne bayan kwana daya da babban sifetan ‘yan sanda IGP Adamu ya sanar da ruguja jami’an sakamakon zanga-zanga da ta barke a wasu sassan Najeriya.

Buhari ya ce gwamnati ta tabbatar da cewa za ta hukunta dukkanin jami’an da aka samu da zaluntar ‘yan Najeriya.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog