Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Karin Albashi: Majalissar Dattijai ta amince da karin albashin N30,000

1 min read

Majalissar Dattawan Najeriya ta amince N30,000 a matsayin sabon albashin ma’aikatan Najeriya.

A kwanakin baya dai kungiyar kwadago ta NLC ta bukaci gwamnati data yiwa ma’aikata karin albashi daga N18,000 zuwa N60,000.

Sai dai gwamnatin Najeriya taki amincewa, yayin data tsaya akan biyan N27,000.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa majalissar dattijan karkashin kwamitin ADHOC, sun rattaba tare da amincewa da biyan N30,000 a matsayin sabon albashin ma’aikata.

Tin dai watan Janairun 2019 majalissar wakilai ta amince da karin albashin a yunkurin data kira na tabbatar da walwalar ma’aikatan Najeriya.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.