(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Paul Pogba ya karyata rade-radin dena buga wa Faransa wasa

Karatun minti 1

Dan wasan kasar Faransa, Paul Labile Pogba ya karyata wasu rahotannin da suka ce ya dena buga wa kasar Faransa wasa.

Wasu rahotanni dai daga jaridar The Sun ta kasar Burtaniya da wasu jaridun gabashin duniya ne suka rawaito cewar Pogba ya dena buga wa kasar wasanni saboda ‘goyon bayan batancin da suka yi wa fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad SAW.

Da yake karyata batun, dan wasan ya ce wannan labarin karya ne kuma shi bai san da shi.

Da safiyar yau, DABO FM ta fitar da rahoton cewar Pogba ya ajiye buga wa kasar wasan, sai dai mun bayyana cewar hukumar kwallon kafan kasar da shi dan wasan basu tabbatar da maganar ba.

Da yake wallafawa a shafinsa na Instagram, Pogba ya ce; “Ni bana goyon bayan ta’addanci ko wane iri ne.

“Zan dauki matakin shari’a a kan wannan abin da wadannan mawallafan da masu yada labarin nan da yake karya dari bisa dari.

“A gaggauce, ina kira ga jaridar The Sun, wasu daga cikin sun je makaranta kuma na san za su tuna yadda malamansu suka rika ce musu su kasance masu tuba tushen magana, kada ku rubuta idan baku da tabbas.”

“Amma yanzu ma kun sake yi kuma a wannan karon ma a maudu’i mai hargitsi, kun ji kunya.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog