Ganduje ya ba wa Mu’azu Magaji tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidajen Kano sabon mukami

dakikun karantawa
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya

An inganta da karfe 4:00 na yamma 29 ga Oktoba 2020.

Gwamnatin Kano ta baiwa tsohon kwamishinan da ta kora, Engr Mu’azu Magaji sabon mukami bayan korarshi da ta yi a matsayin Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewar a ranar 18 ga watan Afrilun 2020 ne dai gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige Engr Mu’azu Magaji daga mukaminsa bayan ya yi wasu kalamai masu kama da murnar mutuwar Mallam Abba Kyari.

Da yake bayyana samun sabon aikin da gwamnan Ganduje ya nada shi a shafin Facebook, Engr Mu’azu ya godiyarsa ga gwamnan bisa sake bashi damar yin aiki a gwamnatinsa.

“Alhamdulillah, na sake samun dama a gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje domin yin aiki a matsayin Shugaban Kwamitin Masana’antu na jihar Kano.”

Kazalika ya sake bayyana cewar ya samu aiki a matsayin shugaban shirin NNPC da zai janyo bututun Iskar Gas da zai taso daga jihar Kogi, ya yanka ta birnin Abuja, Niger, Kaduna ya kuma tsaya a jihar Kano.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da nadin Engr Mu’azu a wata takardar kama aiki da ofishin sakataren gwamnatin jihar ya aike masa da ranar yau Alhamis.

 

Cikin takardar kama aiki ofishin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji ya aike wa Engr Mu’azu, takarda mai lamba SSG/REPA/S/F/59/1 ta ce gwamnatin ta nada shi a matsayin Shugaban Kwamitin da zai jagoranci aiki samar da Bututun Iskar Gas.

“Gwamnan Dr Abdullahi Ganduje ya amince da kafa Kwamitin na tabbatar da aikin sanar da bututun iskar Gas da masana’antun Gas na jihar Kano wanda zai yi aiki da NNPC.”

“Ina sanar da cewa an amince da nada ka a matsayin shugaban Kwamitin.”

An nada Alhaji Kabiru Musa Adamu, shugaban Kungiyar masu kera kayayyaki ta Najeriya reshen Sharada/Chalawa, wanda zai kasance a matsayin mataimakin shugaba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog