Labarai

Sarakunan Zamfara sun kalubalanci Ministan Tsaro ya fadi sunayen masu hannu a rikicin Zamfara

Majalissar Sarakuna da shuwagabannin gargajiya na jihar Zamfara sun bukaci Ministan Tsaron Najeriya, Dan Ali, da ya fadi sunayen Sarakunan da yace da sa hannunsu ake kashe-kashe da sace-sace a Zamfara.

Da yake bayani a madadin majalissar, Sarkin Bagudu, Alhaji Hassan Attahiru, yace ministan ya fito ya fadawa duniya suwaye suke da hannu a ciki.

Sarki Bagudu ya kara da cewa, indai har Ministan Tsaro, Dan Ali ya gaza fitowa ya fadi sunayen Sarakunan, to tabbas maganar batada tushe da asali kuma a iya kiranta da karya.

“Tin shekaru da suka wuce muke bawa jami’an tsaro gudunmawa wajen bada bayanan na daga wuraren buyar ‘yan ta’addar, da bayani game da komai da komai, amma jami’an tsaro sun gaza yin abinda ya dace.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Sarkin Zurmi na Zamfara ne yace a kashe dukkan mutanen Dumburum – Gov Abdul’aziz Yari

Dangalan Muhammad Aliyu

Jihar Zamfara ta rufe dukkanin iyakokinta don kariyar Coronavirus

Aisha Muhammad

Ana ta Rai…: Majalissa dokoki ta aminta da karin sabbin masarautu a jihar Zamfara

Dabo Online

Gwamnatin Zamafara zata dauki matsafa 1,700 domin tabbatar da tsaro

Dangalan Muhammad Aliyu

‘Yan gudun hijira a Zamfara sun fara komawa gidajensu bayan samun ingantuwar tsaro

Dabo Online

Zamafara: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga sama da 20

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2