Kasar Kamaru ta shirya maido da ‘yan gudun hijirar Najeriya mutum 4000

dakikun karantawa

Yan gudun Hijira 4000, yan asalin Najeriya ne zasu dawo gida Najeriya a cewar kwamitin tsare-tsare akan maido da yan gudun hijira zuwa Najeriya daga kasar Kamaru.

Kwamitin ya bayyana cewa ‘yan gudun hijirrar dake zaune a kasar Kamaru, ‘yan jihar Adamawan Najeriya ne.

Mutanen sun tsere zuwa kasar Kamaru bisa dalilin rashin tsaro da akayi ta fama dashi musamman a jihohin yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Sashin Hausa na jaridar Legit.ng ya rawaito cewa; “A lokacin da yake karbar wakilan yan kwamitin a gidan gwamnatin jihar Adamawa dake a Yola, gwamna Ahmadu Umaru Finiri ya bayyana cewa gwamnatinshi a shirye take wajen ganin ta karbi yan gudun hijiran sun dawo gida lafiya.

Ya bayyana cewa gwamnatin a shirye take da ta taimaka wajen ganin an gudanar da aikin maido da yan gudun hijiran inda ya kara da cewa da zarar an maido su za kafa kwamiti da zai tallafa masu.

Fintiri ya yabawa kwamitin da kuma hukumomin kasar Kamaru da suka daukin nauyin kula da yan gudun hijran.

Hajiya Sadiya Umaru Faruq, komishinar gwamnatin tarayya ta hukumar kula da yan gudun hijira ta kasa ta ce sun kai ma gwamna Fintiri ziyarar ne don su sanar dashi akan shirin da sukeyi na maido da ya gudun hijira yan asalin jihar Adamawa dake a Kamaru.

Hajiya Sadiya ta bayyana cewa za su fara aikin maido da yan gudun hijrar kwanannan sa’annan ta roki gwamnatin jihar da ta taimaka masu wajen ganin an gudanar da aikin cikin nasara.” – Hausa Legit.ng

Karin Labarai

Sabbi daga Blog