//
Tuesday, April 7

Mata masu tabin hankali a Najeriya sunfi ‘yan kasar Canada, Morocco da Andalus yawa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Binciken masana lafiya a Najeriya ya nuna cewa daga cikin mutane miliyan 201 ‘yan Najeriya, mutane miliyan 60 ne suke da tabin hankali.

“Ciwon Hauka a Najeriya yana karuwa sosai. Mutane suna kara samun tabin hankali bisa wahalhalun da ake fama dashi a kasar nan. Basu da kudi, mutane da dama suna fadawa shan magani ba tare da umarnin masana na ba. Mutane dayawa suna yiwa giya shan ganganci da ta’ammali da miyagun kwayoyi irinsu Tramol da tabar wiwi.

Daga bakin kwararren likitan kwakwalwa na Asibitin Koyarwa na jami’ar Ilorin, Dr Baba Issa.

Binciken da muka gudanar a nan DaboFM, mun binciko wata kiddidiga da ma’akatar kula da lafiya ta Najeriya fitar tare da kokenta akan lamarin.
Hukumar kula da lafiyar tace kashi 30 daga cikin 100 na adadin mutanen Najeriya suna da tabin hankali.

Masu Alaƙa  Kashi 6 cikin 10 na matan Najeriya, sunada tabin hankali -Masana Kwakwalwa

Su ma a nasu bangaren masana kiwon lafiya sun tabbatar da hakan tare da cewa damuwa, tsanani, kunci da wahalar rayuwa, yana daga cikin abinda yake janyowa kasar yawan masu tabin hankalin.

DaboFM ta binciko cewa daga cikin adadin ‘yan Najeriya miliyan 201, mutane 60,300,000 ne suke da tabin hankalin. Sune kaso 30 na adadin ‘yan Najeriya.

Adadin yawan da Najeriya take su da masu tabin hankali yanada matukar yawa, hakan yasa muka sake binciko wasu kasashe da adadin masu tabin hankali a Najeriya yafi yawan adadin mutane dake rayuwa a kasashen.

Ga jerin wasu daga cikin manyan kasashen duniya da masu tabin hankalin Najeriya sukafi kasar yawa;

Masu Alaƙa  Ko kunsan laifi ne siyar da tabar sigari ɗai-ɗai a Najeriya saboda gurbacewar yara?

Canada tanada mutane miliyan 36, Spaniya, miliyan 46, Morocco, Miliyan 35, Ghana, miliyan 28, da kasar Holland mai mutane miliyan 17.

Bisa binciken da Dr Auwal Sani Salihu na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake jihar Kano ya gudanar, Dr Auwal yace kaso 6 daga cikin 10 na matan Najeriya suna da tabin hankali, inda suk kuma maza suke da kaso 4.

Daga cikin adadin 60,300,000 na masu tabin hankalin na Najeriya, 36,180,000 daga cikinsu Mata ne, 24,120,000 Maza.

Mata suke da kaso 18, Maza kuma nada 12 daga cikin kaso 30 na ‘yan Najeriya masu tabin hankali.Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020