Updated on 26/01/2020.
Ranar 30 ga watan Yuni 2019, Allah Ya karbi rayuwar gogaggen dan jaridar dan asalin jihar Kano.
Marigayi Umar Sa’idu Tudunwada, fitaccen dan jarida na jihar Kano, shugaban mawallafan Najeriya, ya taba wallafa wani rubutu a shafinshi na Facebook, wanda yayi tsokaci akan halayyar mutanen arewa na kin ganin girman gwarzayensu.
DABO FM ta binciko cewa; Marigayi Umar Sa’idu Tudun wada ya wallafa rubutun ne a ranar 6 ga watan Yulin shekarar 2017.
“Matsalar mu ta Kanawa ko ma ince ‘yan Arewa? Bama girmama gwarzayen mu sai bayan mutuwarsshi.
“Dubu dai yadda ake ta yabon Marigayi Danmasanin Kano, amma lokacin da yake raye yawacin masu yabon nasa a yau, zagin sa sukai ta yi lokacin yana raye.
“Allah wadaran irin wannan munafunci. Haka duk gwarzayen mu suka sha fama – Dubi Audu Bako, Murtala Mohammed, Abubakar Rimi da sauransu.
Haka zamu yi kuka Idan su Buhari da Kwankwaso suka tafi. Ina mai matukar zubar da hawaye a kan haka.”
