1
Kasar Saudiyya ta bayyana ranar Asabar, 9 ga watan Agusta a matsayin ranar Arfah
Kotun koli ta kasar Saudiyya ta bayyana ganin sabon watan Dhul-Hijja, inda ta tabbatar da ranar Juma’a a matsayin daya ga wata.
Kotun ta bayyana ranar 9 ga watan Agusta a matsayin ranar fara aikin Hajji, inda kuma ranar 10 ga watan zai kasance ranar Arfa tare da cewa ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta zai kasance ranar Sallah Babba.
Kasar Saudiyya ta bayyana ranar Asabar, 9 ga watan Agusta a matsayin ranar ArfahTini dai kasar ta amsa cewa; Alhazai 1,249,951 ne suka sauka a kasar domin yin aikin Hajjin shekara 2019.
Sai dai har zuwa yanzu kasar Najeriya bata bayyana ganin wata ko sanar da ranar da zata gudanar da ta ta babbar Sallar ta bana.
