Labarai

Kasar Saudiyya taki halartar taron kasashen Musulmi akan yunkurin ceto Musulman China

Kasar Saudiyya taki halartar taron da aka shirya a kasar Malasiya da nufin daukar mataki domin ceto Musulman da ake zargin kasar China da azabtarwa.

Ana dai zargin hukumomi a kasar ta China da tsare musulmai sama da miliyan 1 ‘yan asalin kabilar Uighur a lardin Xinjian.

Zarfin da kasar China ta musanta.

A nata bangaren, kasar Saudiyya tace taki halartar taron bisa shirya taron da sunan kungiyar kasashen Musulumai ta duniya ‘OIC’

Duk da assasa taron da Firaministan kasar Pakistan, Imran Khan yayi, ya janye daga zuwa taron bisa matsin lamba da kasar Saudiyya tayi masa. – Kamar yacce rahotanni suka bayyana.

DABO FM ta tattaro cewa an gudanar da taron ne a birnin Kuala Lumpar, babban birnin kasar Malaysia.

Kasashen da suke basa shiri da Saudiyya irinsu Qatar, Turkiyya da Iran sun samu halartar taron.

Karin Labarai

UA-131299779-2