Labarai

Dambarwar Ganduje da Sarkin Kano Sunusi ta fito da sabon salo

Har yanzu rikicin dake tsakanin gwamnan jihar Kano da mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi, bai dauki hanyar karewa ba sai ma sabon salo da ya fito dashi.

Majiyoyi daga fadar gwamnatin Kano sun bayyana cewa akwai sabbin tarko da gwamnatin zata danawa Sarkin Kano duk da ya karbi mukamin da gwamnatin ta bashi.

Majiyoyin sun ce daga ciki akwai komawa karbar umarnin daga shugaban karamar hukuma a maimakon tunkarar gwamna kai tsaye idan duk wani abu ya taso kamar yacce aka saba.

Haka zalika majiyoyin sun bayyana gwamnatin zata bawa Sarki Sunusi umarnin samawa ragowar Sarakunan jihar guda 4 ofishi a gidan Makama dake jihar ta Kano.

Majiyar tace; “Gwamnati zata bayyana cewa; “Duk sanda Sarkin Kano zai yi wata tafiya, sai ya nemi izini daga shugaban karamar hukumarshi ta Kano Muncipal.”

“Dole Sarkin Kano ya nemawa sauran Sarakunan guda 4 ofishin aiki a Sakatariyar da gwamnati zata samar.”

“Daga cikin wadannan sharuda, duk wanda Sarkin ya ketare, doka zata hukunta shi wanda hakan zai iya sawa a tsige shi.”

A ranar 19 ga watan Disambar 2019, gwamanti ta baiwa mai martaba Sarkin Kano, wa’adin kwanaki biyu akan karba ko kin shugabancin da gwamnan jihar ya bashi na shugabantar Majalissar Sarakunan jihar.

Sai dai bayan kasa da awanni 48, Sarki Muhammadu Sunusi, ya mayarwa da gwamnati takardar karbar shugabancin.

Karin Labarai

Masu Alaka

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Manyan bukatu 5 da Ganduje yake so majalisa ta zartar masa kan masarautar Kano

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje na shirin ayyana Sarkin Bichi a matsayin babban sarki a Kano

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu-Yanzu: An faɗi gabana ana rokon tilas saina tumɓuke rawanin Sarki Sanusi -Ganduje

Muhammad Isma’il Makama

Kotu ta sake dakatar da Ganduje akan kirkirar sabuwar Majalissar Sarkunan Kano

Dabo Online

Sarki Sanusi ya sallaci gawar Sallaman Kano

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2