Tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan
Bincike

Yacce shugaba Jonathan ya kashe biliyan 40 wajen gyaran Majalissar Tarayya a 2013

A makon da muke ciki, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2020 wanda a cikinshi ne ya aminta da kashe Naira biliyan 37 domin gyaran zauren Majalissar Tarayyar Najeriya baki daya.

Lamarin ya janyo cece kuce a kasar bisa yawan kudaden duba da cewa kudaden zasuyi amfani wajen gina abubuwa da dama masu amfani ciki har da gini ajujuwan karatu na zamani guda 10,360. Wanda ake ganin gwamnatin da take kiranta da mai yin gaskiya idan ta aikata haka, bata da bambanci da gwamnatocin baya da take kushewa.

DABO FM ta binciko yacce gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta kashe Naira biliyan 40 wajen gyaran zauren Majalissar a shekarar 2013.

A ranar Laraba, 11 ga watan Disambar 2013, Minsitan Abuja na wancen lokacin, gwamnan jihar Bauchi a yanzu, Sanata Bala Muhammad, ya bayyana yacce gwamnatin tarayya ta amince da kashe biliyan 40 domin gyaran zauren Majalissar.

Bala Muhammad ya bayyana hakan ne a dai dai lokacin da yake magana da manema labarai jim kadan bayan fitowarshi daga zaman majalissar zartawa a ranar ta Laraba.

DABO FM ta tattaro Sanatan ya bayyana cewa; “Zamu rufe duka zaurukan Majalissar tarayya guda biyun na tsawon watanni 12 kuma munyi sa’a muna da manyan dakunan zaman kwamitoci wanda zasu isa a cigaba da gudanar da zaman Majalissun.”

“An ware biliyan 40.238 akan wannan aikin, kuma zai dauke watanni 40 a yinshi.”

Duba shafin Jaridar Vanguard da Daily Trust domin samun tabbacin maganar Sanata Bala Muhammad a wancen lokacin

Sai dai a wancen lokacin gwamnatin ta ware kudin ba iya gyara ba, Sanata Bala Muhammad ya bayyana daga cikin kudin za’a gina zaure 1 da. Ofishin yin kasafin kudi, wajen shan magani, Laburari, dakin taro, dakin kallon Talabijin da jin radiyo, dakin motsa jiki da sauransu.

Rahoton Vanguard – www.vanguardngr.com/2013/12/fec-okays-n40-2bn-national-assembly-complex-renovation-third-phase-construction/

Rahoton Daily Trust – https://www.dailytrust.com.ng/fg-approves-n40bn-to-renovate-national-assembly-complex.html

Karin Labarai

UA-131299779-2