Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewar daliban ajin karshe da zasu kammala karatun Sakandire a bana, ba za su rubuta jarrabawar WAEC ba sakamakon cutar Kwabid-19.
Gwamnatin ta tabbatar da haka ne a zaman majalissar zartarwa na yau Laraba a fadar shugaban kasa ta Aso Villa.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya bayar da sanarwar cewa za a yi jarrabawar a Najeriya.
Babban Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da yake karin haske dangane da batun fasa yin jarrabawar a Najeriya, ya ce babu ranar bude makarantu a Najeriya har sai masana lafiya sun bayar da shaidar cewa al’amuran cutar Kwabid-19 sun daidaita.
Hukumar WAEC dai ta fitar da ranar 15 ga watan Agusta a matsayin ranar da za a fara jarrabawar a kasashen Afrika ta yamma.
Cikakken bayani yana zuwa.
