Labarai

Kayi addu’ar zaman lafiyar Borno yafi kayi tattakin zuwa waje na – Zullum ga mai tattaki

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zullum, yayi kira ga matashin da ya dakatar da tattakin da zai yi zuwa Borno dominshi.

Da yake bayyanawa a shafinshi na Twitter, gwamna Zullum yace mutanen Borno sunfi bukatar addu’ar samun zaman lafiya fiye da tattakin da zaiyi domin tayashi murna da goyon baya.

DABO FM ta tattara cewa matashi mai suna Umar Zubairu ya bayyana fara tattaki daga jihar Jigawa zuwa Borno domin taya gwamnan murnar samun nasarar zabe.

Gwamnan yace; “Na samu labarin wani dan uwa, Umar Zubairu ya fara tattaki daga Jigawa zuwa Borno a dalilina.”

“Usman, lallai na yaba da kokari da goyon bayanka. Ina kuma kira daka dakatar da wannan shirin naka. Ni a waje na ka riga kazo Maiduguri.”

Gwamnan yayi kira ga matashi dama sauran mutane da su sanya jihar Borno dama sauran sassan Najeriya cikin addu’o’insu.

“Ina kira da mu sanya Borno da sauran sassan Najeriya cikin addu’o’inmu da mukeyi a kebance.“

DABO FM ta tattaro gwamna Zulum ya kara da cewar samun goyon baya ta hanyar addu’a yafi ayi tattakin domin nuna goyon baya ko soyayya.

“Goyon baya ta hanyar komawa ga Allah tafi (yin tattaki) tasiri da fa’ida.”

Masu Alaka

Gwamna Zulum ya nada masu bashi shawara 27

Dabo Online
UA-131299779-2