Amarya a Kano ta caccakawa mijinta wuka bayan aurensu da watanni 6

dakikun karantawa

An zargi amaryar dake zama a jihar Kano ta caccakawa mijinta wuka a ciki bayan zamansu na watanni 6.

An zargi Matar mai suna Fatima Musa ta caccakawa mijinta mai suna Sa’eed Muhammad Hussain wukar a cikinshi mai dauke da guba, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

Bisa bincike, DABO FM ta gano yanzu haka Sa’eed Muhammad yana kwance a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano inda yake karbar kulawa daga wajen likitoci a yanayin yanzu.

A nasu bangaren, yan uwan Fatima Musa sun hallara a asibitin Mallam Aminu Kano inda suka bayyana cewa “Yar su bazata taba aikata wannan mummunan aiki ba.”

Sai dai DABO FM ta binciko cewa wasu daga cikin abokan Sa’eed sun bayyana cewa wannan ne karo na 3 da Fatima Musa tayi yunkurin hallaka mijinnata a kasa da watanni 6 na aurensu.

Majiyoyi daga wasu abokan Sa’eed sunce dai an taba kama Fatima Musa da niyyar halaka Sa’eed da zuba masa guba.

Sai dai a tabbatar da babu wata cikakkiyar soyayya mai karfi dake tsakaninsu.

Yanzu haka dai Fatima tana tsare a hannun rundunar ‘yan sandan jihar Kano.

Sai dai bayan tattaunawa da wasu daga cikin bangaren dangin Fatima Musa, sun shaidawa DABO FM cewa hatsari ne ya rutsa dashi kuma babu zancen Fatima ta caccaka masa wuka.

Inda a daya bangaren kuma, bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta, wasu na ganin mijin ne ya dake ta wanda har ya yayyaga mata kaya tare da kumbura mata wasu sassan jikinta.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog