//

Kim Jong Un ya gargadi Amurka a sakon sabuwar shekara.

Karatun minti 1
cc: Daily Express UK

Shugban kasar Koriya ta arewa, Kim Jong Un, a ranar talata, ya bayyana cewa yana fatan yarjejeniyar da aka shimfada ta zaman lafiya a kan makamashin nukiliya da suke yi za ta cigaba da wanzuwa tsakaninsu da kasar Amurka a 2019.

Sai dai shugaban ya gargadi fadar White House, Washington da kada tayi yunkurin gwada hakurin mutanen Koriya ta arewar da matsin lamba da kuma takunkumi.

A jawabinshi na sabuwar shekara (Kim Jong Un), ya ce a shirye yake domin cigaba da tattaunawa da shugaban Amurka, Donald Trump domin samun sakamakon da zai amfani Koriya ta Arewa.

Shugaban ya kara da cewa:

Idan amurka tayi watsi da alkwawuranmu kuma ta cigaba dayi mana barazana da matsin lambar to tabbas zamu fito da wata hanya daban.

Daga karshe ya bukaci kasar Amurkar data dakatar da shirin hadin gwiwar sojoji da suka kulla da takwararta ta Korea ta kudu. Ya kuma yi kira ga Korea ta kudu dasu karfafa alakar dake tsakaninsu (Korea Arewa), ya sha alwashin cigaba da shirye-shiryen ginin ma’aikata da ke Kaesong.

Karfafuwar alakarmu da Korea ta kudu zatayi tasiri sosai in har Amurkan ta cire takunkumin data kakaba mana.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog