Jarumi Kader Khan, ya rasu ne a wani babban asibitin kasar Canada a ranar Litinin, 31 ga watan Disambar 2018.
Jarumin dai ya sha fama da wata matsananciyar rashin lafiya da ta kai shi ga yin jinya har ta tsawon mako 16 zuwa 17 kamar yadda ‘dan jarumin Sarfaraz ta bayyanawa manema labarai.

Khan a cikin film din Vardi
“Mahaifinmu ya tafi ya barmu (ya rasu) da misalin karfe shida na yamma agogon Canada kuma anan Kasar (Canada) za’ayi jana’izar shi saboda anan duka ‘yan uwa da danginmu suke” – Sarfaraz
Za’ayi jana’izar jarumin ne a kasar Canada kamar yacce addinin musulunci ya tanada.
An haifi jarumin a garin Kabul, na Afghanistan, ya fara shirin wasan kwaikwaiyo a fim din Rajesh Khanna a shekarar 1973.
- Ya yi fina-finai masu tarin yawa wanda adadinsu yakai dari uku (300)
- Ya rubuta labaran fina-finai 250.

Khan a cikin film din Dulhe Raja tare da Johnny Lever
Daga cikin manyan fina-finan Jarumin akwai:
- Dharan Veer.
- Ganga Jamuna Saraswati.
- Coolie
- Desh Preeme.
