Labarai

Kimiyya: An samu mamakon ruwa a Dubai bayan anyi dashen gajimare

Dashen gajimare ko ace “Cloud Seedling” a harshen nasara wata kimiyya da fasaha ce da masana suka ‘kirkiro wajen yin amfani da sinadarai domin a samu ko a kirkiri mamakon ruwa a duk lokacin da ake da bukata.

Dabo FM ta samo rahoton shafin Dubailand wadda yake haddaddiyar daular larabawa wanda ta rawaito cewa an samu mamakon ruwan sama wanda dama-daman kasar suka samu ruwa da yakai kimanin yawan miliyan 6.7 a ma’aunin cubic mita.

Wannan ya biyo bayan wani dashen gajimare da akayi a sararin samaniyar haddaddiyar daular larabawan wato dubai.

Hukumar bincike ta sararin samaniya dake kula da dumamar yanayi tayi kira da mazauna kasar dasu guji tafiye tafiye a titinan da suke kusa da tsaunuka, kuma tace akwai barazanar ambaliyar riwa a dama damai.

A mamakon ruwan da aka shafe ranar litinin data gabata anayi yayi yawa wanda manyan motoci kirar SUV ma basu iya tafiya a cikinsa ba.

Masu Alaka

Canada ta roki shugaba Buhari ya tura ‘Yan Najeriya miliyan 1 zuwa kasar

Ko ziyarar Trump ga Kim zata kawo karshen dambarwar kasashen biyu?

Dabo Online

Waiwaye: Lokacin da Iran tayi maraba da hukuncin rataye Saddam Hussain

Dabo Online
UA-131299779-2