Sharhi

Labaran Karya: Auren Shugaba Buhari da Sadiya Faruk ba gaskiya bane

Batun karin auren da shugaba Muhammadu Buhari zai yi, batu ne da ya ja hankalin mutanen Najeriya baki daya musamman a Arewacin Najeriya.

DABO FM ta gudanar da bincike domin bin bahasi da niyyar samun sahihin zance kan batun auren shugaba Buhari da Minista Sadiya Umar Faruk.

Binciken ya tabbatar mana da cewa; Labarin na karya ne kuma anayin hakan domin cimma wata manufa da ba’asan mashiryanshi ba.

Babu wata madogara ta gaskiya, daga bangaren Gwamnati ko Iyalansu, da ta gaskata lamarin.

Sai dai masu sharhi a Arewacin Najeriya, suna ganin an kirkiri jita-jitan ne domin hana Minista Sadiya Faruk, yin ayyukanta da suka dace.

Ma’aikatar Minista Sadiya Faruk, sabuwar ma’aikatace da aka kafa ta domin jin dadi da kula da walwalar al’ummar Najeriya musamman wuraren da ake fama da tashe-tashen hankula, wadanda 90 cikin 100 duk jihohin Arewa ne.

Idan akayi duba, za’a ga cewa; mutanen Arewa, zasu fi amfana da ma’aikatar bisa dalilin rashin kwanciyar hankali a yankin.

Kirkirar labarin tana soyayya da Buhari, hakan zai yi abubuwa kamar haka;

Kodai ya hanata katabus na gudanar da ayyukan ta, ko kuma ya hadata fada da shugaba Buhari akan cewa itace take shirya jita-jita domin neman ya Aure ta.

A gefe guda, Uwargidan shugaba Buhari, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, zata nade kafar wando da ita, ta ja runduna domin yaki da ita.

Wanda hakan zai saka ayyukan ma’aikatar suki tafiya har ‘yan Arewa su ki amfana daga ma’aikatar.

Sharhi ne kawai, hakan zai iya sabawa daga yacce wasu zasu kalli lamarin.

Masu Alaka

Adadin ‘yan Najeriya dake son satar kudin kasa yafi na wadanda suka sace da masu sata a yanzu

Dabo Online

Iyalan Marigayi Ado Bayero da Mal Shekarau zasu nemi hakkokinsu na sharrin kisan Sheikh Jafar?

Dabo Online
UA-131299779-2