Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Shin da gaske Shugaba Buhari zai kara aure?

1 min read

Batun karin auren da shugaba Muhammadu Buhari zai yi, batu ne da ya ja hankalin mutanen Najeriya baki daya.

Tin bayan da uwargidan shugaba Buhari, Aisha Muhammadu Buhari, ta shafe tsawon watanni 2 bata zama a fadar gwamnatin dake Abuja, zancen karin auren shugaba Buhari ya fara fitowa, har aka fara alakanta rashin zamanta da zafin tsananin kishin karin auren da shugaban zaiyi tare da zamewarta saniyar ware a cikin gwamnatin. – Sai dai gwamnatin tarayya ta karyata batun.

Wasu daga cikin Jaridun yanar gizo-gizo na Najeriya, sun rawaito cewa; a gobe Juma’a, 11 ga watan Oktobar 2019, shugaba Buhari zai angwance da Minista Sadiya Umar Faruk a babban Masallacin tarayyar Najeriya dake Abuja.

Sai dai daga bangaren Gwamnatin, ta hannu daya daga cikin jami’in watsa labaran shugaba Buhari, Bashir Ahmad, ya karyata lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin “Jita-jita zancen banza.”

Ya kuma kara da cewa; “Hausawa sunce rana bata karya.”

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.