Fada ya kaure tsakanin masu garkuwa da mutane a titin Kaduna-Abuja, sun karkashe junansu

Karatun minti 1

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya sun bayyana cewa fada ya kaure tsakanin ‘yan bindigar da suke garkuwa da mutane a kan titin Kaduna-Abuja da su da abokan ta’addancinsu.

Gwamnatin jihar ta hannun kwamishanan tsaron jihar,  Sameul Aruwan ya shaida cewa jami’an tsaro sun tabbatar da cewa yan bindigar sun kashe Nasiru Kachalla a wani rikici da ya barke tsakaninsu da wasu guggun ‘yan ta’addar.

Nasiru Kacallah dai wani kasurgumin dan ta’adda ne  yake jagorantar ayyukan ta’addanci a hanyar Kaduna-Abuja, baya ga garkuwa da mutane, ana zarginsa da kashe mutane, sace-sace shanu da jagorantar ‘yan bindiga dadi su far wa jama’a.

Kwamishinan ya ce fadan ya kaure ne a ya yin da ‘yan ta’addar suke kason wasu shanun sata tsakaninsu. Ya ce an yi fadan ne tsakanin Nasiru Kacalla da wasu masu aikata irin ta’addansu a dajin da ke kan iyakar Kajuru da Chikun.

“Rikicin ya faru ne a wani dajin kan iyakar kananan hukumomin Kajuru da Chikun. Rikicin da rabon wasu shanun sata ya haifar.”

“Kachalla da mutanensa ne ke da hannu a wasu manyan migayun laifufuka da aka aikata musamman na  garkuwa da mutane Kaduna-Abuja.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog