Kokarin gwamnati na samar da basuka ga manoma abun a yaba ne-Mai Shinkafa

dakikun karantawa

An yaba ma gwamantin tarayya da Babban Bankin Kasa CBN da kuma ma’aikatar aikin Gona bisa kokarin da su ke domin habbaka aikin Noma a Najeriya.

Shugaban Kungiyar manoma Masara ta shiyyar Arewa maso Yamma Alhaji Kabiru Salihu Mai Shinkafa ya bayyana hakan, da yake zantawa da manema labarai game da cigaban da aka samu a bangaren bunkasa harkar noma a kasar nan.

Ya ce, irin kokarin gwamnati na samar da rance mai saukin biya ga manoma da kuma hana shigowa da hatsi ta iyakokin kasar nan ya taimaka wurin habaka amfani da ake shukawa a Najeriya.

Sai dai ya ce duk da cikas da ake samu musamman wurin maido da rancen da aka ba manoma, haka bai sa gwamanti kasa a gwiwa ba wurin kara kaimi a kan harkar noma. Ko a Jihar Kaduna kadai, a bana manoma 6,361 ne su ka amfana da rancen gwamnati akan inganta harkar noman masara.

A cewar shi, irin albarkar kasa da Allah ya wadata yankin Arewacin Najeriya, akwai takaici kan yadda wasu ke kokarin wofantar da Ni’imar da Allah ya yi ma Arewa na kin amfani da kasar Noma da suke da shi kuma ka ji ana kukan talauci.
Sai ya naimi gwamnatoci a kowanne mataki da mawadata da ma kungiyoyi su yi duk mai yiwuwa domin samar da masana’antun sarrafa hatsi a Arewa.

“tun da a yau kashi 75 cikin dari na masara da ake nomawa a kasar nan ana sarrafa shi ne domin samar da wani nau’in abinci da za’a yi amfani da shi, Amma duk da wannan kokarin akan samu koma baya musamman a yankunan da ya kamata a ce ana habbaka aikin gona domin samar da abun da ake bukata bangaren hatsi”, a cewar Kabir Salihu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog